Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ofishin Hulɗa da Jama'a na Jami'ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Hormozgan Nan da nan bayan faruwar wannan lamari, dukkan ma'aikatan agaji da na jinya na Jami'ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Hormozgan sun kasance cikin shiri na cikakken lokaci, kuma ana ci gaba da daukar matakan jinya da suka dace don jinyar wadanda suka jikkata.
Sannan an jiyo ƙarar fashe-fashe 8 a yankin kauyen Masen da ke tsibirin Qeshm, biyo bayan harin sama da Amurka ta kai
A yammacin yau ma, wani makami mai linzami na makiya ya faɗi a wannan kauyen na Qeshm.
A wani rahoton mutanen yankin Iranshahr sun ji karar fashe-fashe mai karfi guda uku a kusa da filin jirgin sama na Iranshahr, kuma rahotannin mazauna yankin sun nuna an kai wani mummunan hari a filin jirgin.
Har yanzu ba a samu bayanin adadin barnar da wadannan hare-haren suka haddasu ba, amma jami'an ayyuka na sojojin da ke yankin a halin yanzu suna nan a wurin filin jirgin.
Sannan bisa ga rahotannin da aka samu, 'yan mintuna da suka wuce an ji karar fashe-fashe da dama a kewayen garin Hamidiyeh
Sannan Amurka ta kai hari kan gadar Bandar Khamir
Da misalin karfe 11 na daren yau, gadar Kahouristan da ke gundumar Bandar Khamir, wadda ita ce hanyar haɗi tsakanin Bandar Abbas da Lar, ta fuskanci harin makiya Amurka.
Ma'aikatan kula da hanyoyi suna shirya wata hanya maimakon wannan hanyar haɗi.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa a lokacin da makamin ya fado kan gadar, motoci masu wucewa suna kan gadar, amma har yanzu babu wani bayani game da adadin asarar rayuka
A ɓangaren ta ita ma Iran ta fara kai hare-haren ramuwa inda ta kai hare-hare a ƙasar
Kamar yadda kafofin watsa labarai suka faɗa cewa an ji yo fashe-fashe masu tsanani a ƙasar Kuwait
Sojojin Kuwait a daren Alhamis sun yi iƙirarin cewa sun gano tare da kakkabo jirage marasa matuki 32 a sararin samaniyar ƙasarsu.
Ra'ayinka